Mu da muka yi wahala ne ya kamata mu jagoranci majalisa - Gudaji Kazaure

Mu da muka yi wahala ne ya kamata mu jagoranci majalisa - Gudaji Kazaure

Sabon rikici na shirin kunno kai a majalisar dokokin kasar kan wadanda za su shugabancin majalisar, inda wasu yan majalisar da dama suka nuna adawa da tsarin ware mukami ga wani bangare.

Hon Gudaji Kazaure daya daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai kuma babban dan kashenin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nuna rashin goyon bayan kebe mukami ga wata shiyya illa a baje koli mai rabo ya samu.

Dan majalisar ya bayyana cewa yana nan kan bakarsa ta neman kujerar kakakin majalisar wakilai, sannan kuma cewa zai nemi goyon baya daga 'yan uwansa 'yan majalisa domin su zabe shi.

Jam`iyyar APC da ke da rinjaye na neman hada kan 'ya'yanta ne don mamaye dukkan manyan mukaman da ke sabbin majalisun dokokin da za a kafa, kasancewarsu masu rinjaye.

Mu da muka yi wahala ne ya kamata mu jagoranci majalisa - Gudaji Kazaure
Mu da muka yi wahala ne ya kamata mu jagoranci majalisa - Gudaji Kazaure
Asali: Facebook

APC na son kaucewa barakar da ta samu a shekara ta 2015, inda jam`iyyar hamayya ta PDP ta shammace ta har ta mamayi kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Hon Gudaji Kazaure ya ce ya ja kunnen APC cewa idan ba a yi hattara ba abin da ya faru a 2015 yana iya sake faruwa a bana.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya billo yayinda Ndume ya nuna adawa da zabar Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

Ya yi kira ga shugaban kasa Buhari ya diba magoya bayansa irinsa wadanda ba za su bari a saba ma shi ba.

"Ba yanda za a yi ace an ci yaki an yi nasara amma idan an zo kason ganima ace ba za a fara duba wadanda suka fi shan wahala da yin biyayya," in ji shi.

Ya kara cewa ya kamata a duba a ga wadanda suka fi jajircewa a ba su shugabancin majalisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel