Ka amince da sakamakon zabe - Babban jigon APC ga Atiku

Ka amince da sakamakon zabe - Babban jigon APC ga Atiku

- Wani babban jigon jam’iyyar APC a jihar Delta, Kwamrad Durice Jonathan Orugoh ya bukaci dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da ya amince da sakamakon zabe a matsayinsa na mai kishin kasa

- Orughoh ya bukaci Atiku da ya bar batun yawan kuri'un Kano domin shima ya samu kuri'u masu yawa a jihar Delta

Wani babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta, Kwamrad Durice Jonathan Orugoh ya bukaci dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar da ya amince da sakamakon zabe a matsayinsa na mai kishin kasa.

Orughoh ya bayyana rokon ne a wani jawabi da ya gabatar jiya Talata, 26 ga watan Maris a Warri, inda yake cewa yana mamakin dalilin da yasa Atiku ya tsananta kuri’un jihar Kano ga jam’iyyar APC bayan jam’iyyar PDP ma ta samu kuri’u masu yawa daga jihar Delta.

Ka amince da sakamakon zabe - Babban jigon APC ga Atiku
Ka amince da sakamakon zabe - Babban jigon APC ga Atiku
Asali: Twitter

Yace “ko da yake jam’iyyar APC bata yi nasara ba a jihar Delta, jam’iyyar za ta fito da karfinta a 2023 don share jam’iyyar PDP mai ci saboda bata yiwuwa jihar Delta ta kasance a jam’iyyar adawa ga Gwamnatin Tarayya”.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya billo yayinda Ndume ya nuna adawa da zabar Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, a ranar Laraba, kotun daukaka da ke zaman ta a garin Abuja za ta fara sauraron korafi na kalubalantar sakamakon zabe da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar ma ta.

Atiku Abubakar, da ya kasance tsohon mataimaikin shugaban kasar Najeriya, na ci gaba da rashin amincewa tare da kalubalantar sakamakon zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel