Rikici ya billo yayinda Ndume ya nuna adawa da zabar Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

Rikici ya billo yayinda Ndume ya nuna adawa da zabar Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na iya fuskantar wani babban rikici a wajen zabar Shugaban majalisar dokokin kasar, yayinda daya daga cikin yan takarar kujerar majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, a jiya Talata, 26 ga watan Maris, ya caccaki batun zabar Shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Ahmad Lawan, da majalisar ke shirin yi.

A bangare guda, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jiya (Talata) suka ce duk wani zababben sanata na da iko da kundin tsarin mulki ta bashi na tsayawa takarar Shugaban majalisar dattawa, idan aka rantsar da ita a watan Yuni.

Hakazalika, babban jam’iyyar adawa ta bayyana ikirarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban jam’iyyar APC, Mista Adams Oshiomhole na cewa sugabancin majalisa da na kwamitocin majalisar dokokin hakkin APC ne a matsayin “abun dariya da kuma tseren kawai.”

Rikici ya billo yayinda Ndume ya nuna adawa da zabar Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa
Rikici ya billo yayinda Ndume ya nuna adawa da zabar Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa
Asali: Depositphotos

Ndume mai wakiltan kudancin Borno a karkashin jam’iyyar APC, ya fada ma manema labarai a kwatas din yan majalisa da ke Abuja cewa lamuncewa Lawan da Femi Gbajabiamila da Shugaban APC yayi a daren ranar Litinin, a matsayin Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai ya kasance abun kunya da kuma saba ma kundin tsarin mulki.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da hannu a rikicin siyasar jihar Kano - Kwankwaso

Yace: “Abunda ya wakana a wajen taron cin abincin dare a fadar Shugaban kasa a Asorock a daren ranar Litin, inda Oshiomhole, Shugaban APC ya sanar da Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila a matsayin shugabannin majalisun dokokin kasar ya zo mana a bazata daga ni har abokan aikina da dama."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel