Lauya ya yi barazanar maka Kamfanin NNPC a kotun kan daukan ma'aikata

Lauya ya yi barazanar maka Kamfanin NNPC a kotun kan daukan ma'aikata

A yayin da kamfanin man fetur na kasa watau NNPC ya shimfida ma'auni na shekaru a shirye-shiryen sa na daukar ma'aikata, wani Lauya mazaunin garin Abuja, Mista Pelumi Olajengbesi, ya yi barazanar maka sa a kotu.

Cikin wata wasika da ya aike da ita zuwa ga shugaban kamfanin NNPC na kasa, Dakta Maikanti Baru, Olajengbesi ya yi barazanar maka babban kamfanin a gaban kotu sakamakon yadda ya gindaya shekaru a matsayin ma'auni na daukar aiki.

Shugaban Kamfanin NNPC na kasa; Dakta Maikanti Baru
Shugaban Kamfanin NNPC na kasa; Dakta Maikanti Baru
Asali: UGC

A kwana-kwanan nan kamfanin NNPC ya shellanta gayyatar masu sha'awar samun aiki a matakai daban-daban tare da shimfida ma'auni na kada masu neman aikin su haura shekaru 28 na haihuwa.

A sakamakon kishi wannan sharadi na Kamfanin NNPC ya ciwa Olajengbesi Tuwo a kwarya matuka, inda ya kafa hujja da sashe na 3 cikin dokokin kare hakkin dan Adam a Najeriya da ke haramcin nuna wariya ta fuskar ma'auni na shekaru.

KARANTA KUMA: Dan takarar jam'iyyar PDM ya nemi a sake zaben shugaban kasa

Da yake ci gaba da kalubalantar wannan sharadi, Olajengbesi ya hikaito yadda sashe na 42 cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi haramci na nuna wariyar shekaru a kowace ma'aikata yayin bayar da aikin yi ga ma su nema 'yan kasar Najeriya.

Ya ce a yayin da kamfanin NNPC ke karkashin kulawa ta akalar gwamnatin tarayyar Najeriya, akwai bukatar ya kasance mai kare martabar wannan dokoki da kuma hukuncin da kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi yayin mu'amalantar al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel