Dan takarar jam'iyyar PDM ya nemi a sake zaben shugaban kasa

Dan takarar jam'iyyar PDM ya nemi a sake zaben shugaban kasa

Tsugunno na neman yankewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDM, Fasto Aminchi Habu, ya maka shi gaban kotun daukaka kara tare da jam'iyyar sa ta APC da kuma hukumar zabe.

Fasto Habu wanda ya kasance babban Limanin Cocin Northern Evangelism na The Lord's Chosen Charismatic Revival Ministries, ya shigar da korafin sa gaban kotun daukaka kara da aka tanada domin zabe kan zargin ababe na rashin adalci da suka wakana a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Cikin bukatun da ya gabatar babban Limamin na neman kotun daukaka kara ta soke nasarar shugaban kasa Buhari da jam'iyyar sa ta APC tare da neman hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta sake gudanar da wani sabon zabe na kujerar shugaban kasa.

Dan takarar jam'iyyar PDM ya nemi a sake zaben shugaban kasa
Dan takarar jam'iyyar PDM ya nemi a sake zaben shugaban kasa
Asali: Twitter

Korafin Fasto Habu ya bayu ne a sakamakon ikirarin rashin adalci da hukumar INEC ta yi masa na rashin sanya sunan sa da kuma na jam'iyyar sa daga cikin jeranto na takardun zabe da hakan ya yi sanadiyar haramta ma sa takara a babban zabe na bana.

Korafin sa mai lamba CA/PEPC/004/2019 da ya shigar tun a ranar 19 ga watan Maris na 2019, dan takarar na jam'iyyar PDM ya bayyana bakin cikin sa dangane da yadda hukumar INEC ta zame masa ciwon ido bayan ya batar da dukumar dukiya wajen gudanar da yakin neman zabe.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya sun sayi katin wayar salula na N767.23bn cikin watanni uku - NCC

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, bayan bukatar sanya shie cikin jerin 'yan takara, sauran bukatu da Fasto Habu ya gabatar a gaban kotun daukaka kara sun hadar da; soke hukuncin tabbatar da nasarar zabe ga shugaban kasa Buhari, tilastawa hukumar INEC sake gudanar da zaben kujerar shugaban kasa nan da kwanaki 90.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel