Ta'addanci da sayen kuri'u sun dabaibaye zaben cike gibi na gwamnan jihar Kano - EU

Ta'addanci da sayen kuri'u sun dabaibaye zaben cike gibi na gwamnan jihar Kano - EU

Kafar watsa labarai ta Radio France International, RFI, ta ruwaito cewa kungiyar tarayya turai ta muzanta ababen tur da Allah wadai na ta'addanci, sayen kuri'u da kuma firgita al'umma da su ka yi tasiri yayin gudanar da zaben cike gibi na gwamnan jihar Kano.

Kungiyar tarayyar Turai Masu sanya idanun lura kan babban zaben Najeriya na bana, ta ce hauragiya ta tashin-tashina, sayen kuri'u da kuma tayar da hankullan al'umma sun yiwa zaben cike gibi na jihar Kano dabaibayi tare da tasiri yayin gudanar sa a karshen makon da ya gabata.

Ganduje da Abba Kabir Yusuf
Ganduje da Abba Kabir Yusuf
Asali: UGC

Kungiyar Turawan ta kausasa harshe tare da bayyana damuwa kwarai da aniyya kan sakaci na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC da kuma hukumomin tsaro musamman jami'an 'yan sanda na gaza magance matsalolin da aka fuskanta yayin gudanar da zaben a jihar Kano.

Cikin rahoton da kungiyar EU ta fitar kuma wassafa, ta bayyana cewa wakilanta sun yi shaidar yadda 'yan daba da sara-suka rike da makamai na gorori da adduna suka ci Karen su ba bu babbaka wajen firgitar da manema labarai da kuma masu kada kuri'u.

Ta ce 'yan ta'ada da masu tayar da zaune tsaye sun muzgunawa al'umma musamman a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa tare da haifar da tarnaki da ya haramtawa 'yan jaridu gudanar da ayyukan su cikin tsanaki.

KARANTA KUMA: Kalubalai 5 da Gwamna Ganduje zai fuskanta a jihar Kano

Sai dai duk da aukuwar wannan ababe masu cin karo da tsari na dimokuradiyyar, hukumar INEC ta yi gaban kanta na shellantawa tare da tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Kano domin ci gaba da jagorancin a karo na biyu.

Hukumar INEC ta bayyana cewa, biyo bayan kammala zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris, Gwamna Ganduje ya yi nasara yayin da ya lallasa babban abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel