Kalubalai 5 da Gwamna Ganduje zai fuskanta a jihar Kano

Kalubalai 5 da Gwamna Ganduje zai fuskanta a jihar Kano

A karshen makon da ya gabata hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta shellanta tare da tabbatar da nasarar Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka kammala a ranar 23 ga watan Maris.

Gabanin kammalar zaben, hukumar INEC ta gudanar da ainihin zaben a ranar 9 ga watan Maris inda ta kaddamar da hukuncin rashin kammalar sa a sanadiyar adadi na yawan kuri'u da aka soke da ka iya tasiri wajen rinjayar da sakamakon zaben.

Kalubalai 5 da Gwamna Ganduje zai fuskanta a jihar Kano

Kalubalai 5 da Gwamna Ganduje zai fuskanta a jihar Kano
Source: Depositphotos

Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Ganduje yayin da ya lallasa babban abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf. Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a jihar Kano da kuma kasa baki daya sakamakon ababen da suka wakana yayin gudanar da zaben na cike gibi.

Da yawa daga cikin gama garin Mutane, shugabanni, masu fada a ji da kuma kungiyoyi masu kare hakkin bil Adama, sun bayyana rashin jin dadin su dangane da yadda ta'addanci ya dabaibaye zaben cike gibi da hukumar INEC ta gudanar a wasu yankunan jihar Kano.

KARANTA KUMA: Ezekwesili ta samu kyautar Forbes ta Mace mai tasiri a zamantakewar Afirka

A yayin da rashin tsaro ya mamaye zaben jihar Kano musamman yadda hukumomin tsaro suka gaza wanzar da zaman lafiya a sakamakon juya baya da al'umma suka yiwa gwamna Ganduje, akwai yiwuwar zai fuskanci kalubalai daban-daban a wa'adin sa na biyu.

Kafar watsa labarai ta BBC Hausa ta ruwaito cewa, yayin da zaben gwamnan jihar Kano ya kasance mafi daukar hankali cikin dukkanin zabukan da aka gudanar a fadin Najeriya, akwai wasu manyan kalubalai biyar da gwamna Ganduje zai runguma a bisa kujerar sa ta mulki.

Ga jerin su kamar haka:

1. Rashin tsaro

2. Rarrabuwar kawunan al'umma

3. Yaki da Jahilci

4. Tagayyara ta rayuwar al'umma

5. Zabar abokanan tafiya da Hadimai macancanta

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel