Ezekwesili ta samu kyautar Forbes ta Mace mai tasiri a zamantakewar Afirka

Ezekwesili ta samu kyautar Forbes ta Mace mai tasiri a zamantakewar Afirka

Tsohuwar 'yar takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar ACPN, Oby Ezekwesili, ta ciri tutar samun lambar yabo yayin da ta lashe kyautar mujallar Forbes ta Mace mai tasiri a zamantakewar nahiyyar Afirka.

Mujallar Forbes ta duniya mai rabe-rabe tsakanin zare da abawa, ta yiwa Misis Ezekwesili gagarumar kyauta ta saon barka yayin bikin bayar da kyaututtuka ta Forbes Woman Africa Awards da aka gudanar cikin birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu a kwanan nan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, Ezekwesili ta samu wannan lambar yabo a sanadiyar yakin Bring Back Our Girls da ta assassa a zaurukan sada zumunta na sai an dawo da 'yan Matan Chibok da Mayakan Boko Haram su ka yashe a gwamnatin baya ta Goodluck Jonathan.

Oby Ezekwesili
Oby Ezekwesili
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan yaki na fafutikar dawo da 'yan Matan Chibok da Misis Ezekwesi ta assassa ya samu karbuwa da goyon baya a duk wata kafa ta dandalan sada zumunta na duniya.

Sauran Matan nahiyyar Afirka suka samun tukwicin mujallar Forbes tare da cirar tuta gami da samun lambar yabo a fannikan wasanni, kasuwanci, kimiyya, nishadantarwa da kuma jagoranci sun hadar da Divine Simbi-Ndhlukula, Rachel Simbande, Caster Semenya, Sho Madjozi, Uche Pedro da saurancu.

KARANTA KUMA: An gano kuskure a sakamakon zaben da Atiku ya binciko daga yanar gizon hukumar INEC

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, Ezekwesili da kasance tsohuwar Ministan ilimi a Najeriya ta alakanta janye takarar ta kujerar shugaban kasa gabanin babban zabe domin kare mutunci da kuma martabar kanta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel