An gano kuskure a sakamakon zaben da Atiku ya binciko daga yanar gizon hukumar INEC

An gano kuskure a sakamakon zaben da Atiku ya binciko daga yanar gizon hukumar INEC

A yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon zabe, Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar na ranar 23 ga watan Fabrairu, ya gabatar da wani sakamakon zaben da ya bankado shi daga yanar gizon hukumar zabe ta INEC.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa da gamayyar kuri'u 15,191,847.

Sai dai yayin da hukumar INEC ta tabbatar da shan kayen Atiku bayan ya lashe kuri'u 11,262,978, ya hau kujerar naki ta amincewa da sakamakon zaben da cewar shi ke da rinjayen nasara da kuri'u 18,356,732 yayin da a cewar sa Buhari ya samu kuri'u 16,741,430.

An gano kura-kurai a sakamakon zaben da Atiku ya binciko daga yanar gizon hukumar INEC
An gano kura-kurai a sakamakon zaben da Atiku ya binciko daga yanar gizon hukumar INEC
Asali: Twitter

Duk da cewar sakamakon bai hadar da kuri'un jihar Ribas ba, Atiku ya gabatar da wannan sakamako a gaban kotun daukaka kara da ya yi ikirarin ya binciko ta barauniyar hanya daga ma'adanan yanar gizo na hukumar INEC.

Binciken manema labarai na jaridar Premium Times ya gano cewa, sakamakon zaben da Atiku ya gabatar cike ya ke da kura-kurai da suka hadar da cewar takarar kujerar shugaban kasa ta gudana ne kurum tamkar tsakanin sa da shugaba Buhari ba tare da sauran 'yan takara kimanin 70 da suka fafata a zaben ba.

Cikin sakamakon zaben da Atiku ya gabatar, ba bu kuri'a ko daya da aka soke cikin sakamakon zaben jihohi 33, kazalika sauran 'yan takara 71 da suka fafata a zaben ba su samu ko da kuri'a guda ba.

KARANTA KUMA: A binciki ta'addancin da ya auku yayin zabe a jihar Kano - Amnesty

A jihohin Abia, Bauchi da kuma Cross River, sakamakon zaben da Atiku ya gabatar na nuni da cewa adadin kuri'u da aka kada tsakanin sa da shugaba Buhari sun haura adadi na yawan masu kada kuri'a da hukumar INEC ta tantance.

A yayin da jam'iyya mai ci ta APC ta mai she da ikirarin Atiku a matsayin bankaura da kuma hauragiya ta mafarki, ya na ci gaba da dagiya kan samun nasara ta lallasa Buhari da tazara ta kimanin kuri'u miliyan 1.6.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel