A binciki ta'addancin da ya auku yayin zabe a jihar Kano - Amnesty

A binciki ta'addancin da ya auku yayin zabe a jihar Kano - Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya akan ta binciki ta'addanci da ya auku yayin zaben cike gibi na gwamnan jihar Kano da aka gudanar a makon da ya gabata.

Amnesty International ta yi kiran gaggawa na neman gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike diddigi akan zargin yadda 'yan daba da sara-suka suka kai hari kan manema labarai da kuma gama garin al'umma ma su yunkurin kada kuri'un su yayin zaben gwamna a jihar Kano.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kakakin kungiyar Amnesty, Isa Sanusi, shi ne ya yi wannan kira yayin ganawa da manema labarai na jaridar BBC Hausa a birnin Damaturu na jihar Yobe.

Buhari tare da gwamnan Kano, Ganduje
Buhari tare da gwamnan Kano, Ganduje
Asali: Twitter

Kungiyar mai fafutikar kare hakkin bil Adama ta tur da mummunan lamari na ta'addanci da ya auku yayin zaben cike gibi da aka gudanar a birnin Kano musamman hare-haren da 'yan daba da sara-suka suka zartar musamman akan manema labarai da masu kada kuri'u.

Ta yi kira na neman shugaban kasa Muhammadu Buhari akan gaggauta gudanar da bincike cikin wannan mummunan lamari na abin kunya ga gwamnatin sa da kuma kasar Najeriya baki daya da ya cancanci hukunci na shari'a.

Hukumar zabe ta kasa INEC ta gudanar da zabukan cike gibi na gwamnonin jihar Bauchi, Benewai, Kano, Filato da kuma Sakkwato a matsayin karashin zaben kujerar gwamnan da gudanar a ranar 9 ga watan Maris biyo bayan hukuncin rashin kammalar zabe da ta kaddamar.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a karshen makon da ya shude hukumar INEC ta kaddamar tare da shellanta nasarar Abdullah Umar Ganduje na jam'iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

KARANTA KUMA: Tsagerancin 'Yan siyasa ya sa Sojoji suka mu'amalanci zaben 2019 - Felix Omobude

A ranar Litinin kungiyar tarayyar Turai mai sanya idanun lura akan yadda zabukan Najeriya suka gudana a bana, ta bayyana rashin jin dadi sakamakon yadda ta yi shaidar ababen ta'ada da suka mamaye zaben cike gurbi musamman a jihar Kano, Bauchi da kuma Benuwai.

Kungiyar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito ta bayyana cewa, ta gaza sa ido akan yadda zaben ya gudana cikin mafi akasarin rumfunan zabe a jihar Kano sakamakon yadda 'yan daba rike da gorori da adduna suka ci Karen su ba bu babbaka a karaar hukumar Nasarawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel