Super Eagles ta samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 bayan lallasa Masar

Super Eagles ta samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 bayan lallasa Masar

- Zakarun kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles sun samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 daga hannun gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta

- Haka zalika mai horas da kungiyar kwallon kafar Gernot Rohr ya samu kyautar $10,000 daga gwamnan

- Super Eagles za su buga wasan abota guda biyu a wata Yuni karkashin inuwar FIFA a yayin fuskantar AFCON karo na 32 a Masar

Yan wasan kungiyar kwalllon kafa ta Super Eagles sun samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 daga gwamna Ifeanyi Arthur Okowa na jihar Delta a ranar Tala, 26 ga watan Maris a matsayin ihisani kan nasarar da suka samu akan kungiyar kwallon kafa ta Seychelles’ Pirates a wasan karshe na share fagen shiga gasar kofin nahiyar Afrika (AFCON) da kuma lallasa kungiyar Masar a wasan abota da suka yi.

Fashin baki kan kudaden da aka raba kamar yadda Thenff.com ta wallafa, ya bayyana cewa gwamnan jihar ya kuma yiwa mai horas da kungiyar ta Super Eaglles, Gernot Rohr $10,000, yayin da 'yan wasan suka samu kason $50,000.

Wani abun farin cikin shine, Gwamna Okowa ya kuma yiwa Eagles ihisani bisa kokarinsu na tsallake gasar sharar fagen shiga gasar kofin AFCON 2019 bayan tashi 1-1 da kungiyar kwallon kafa ta Afrika ta Kudu a shekarar da ta gabata, wanda ya biyo da wasanta da Uganda Cranes bayan kwanaki ukku a Asaba.

KARANTA WANNAN: Masu shigo da kaya daga kasashen waje ke nakasa Nigeria - Ogbeh

Super Eagles ta samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 bayan lallasa Masar
Super Eagles ta samu kyautar zunzurutun kudi har $60,000 bayan lallasa Masar
Asali: Original

Kungiyar kwallon kafar baya ga jinjinawa gwamna Okowa bisa wannan gudunmowa da ya yi mata da ma wasan kwallon kafa na Nigeria gaba daya, kungiyar ta kuma jinjinawa keftin din Super Eagles Ahmed Musa na rabawa Dream Team VII N4m bayan nasararsu da Libya, wasan da aka tashi 4-0.

Wannan kuwa ya zama cika alkawarinsa na cewar zai bayar da kyautar N1m ga duk kwallon da kungiyar kwallon kafar ta sha a ziyarar da ya kaiwa 'yan wasan a ranar Asabar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel