Rashin albashi yayi sanadiyyar mutuwar wani Ma’aikaci a Jihar Kogi

Rashin albashi yayi sanadiyyar mutuwar wani Ma’aikaci a Jihar Kogi

Jaridar Daily Trust ta rahoto mana cewa Ma’aikatan bangaren shari’a a jihar Kogi sun shiga cikin wani hali na juyayi da zaman makoki bayan da wani babban Ma’aikacin karamin kotun majistare ya rasu.

Mista Zekery Aguye wanda shi ne mataimakin shugaban wani kotun majistare ya bar Duniya bayan ‘yar rashin lafiya kwanan nan. Zekery Aguye ya cika ne a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Garin Abuja kwanan nan.

Shugaban babban kotun tarayya na Kogi, Yahaya Adamu, ya tabbatar mana da rasuwar Abokin aikin na sa Zekery Aguye inda yake cewa Aguye wanda ya san aiki, ya rasu ne a sanadiyyar gaza daukar nauyin maganin rashin lafiyar.

KU KARANTA: Gudawa ya kama Hadiman Gwamna a sanadiyyar cin abincin waje

Rashin albashi yayi sanadiyyar mutuwar wani Ma’aikaci a Jihar Kogi
Gwamna Yahaya Bello yayi watanni 9 bai biya wasu Ma’aikata albashi ba
Asali: Facebook

Mista Yahaya Adamu ya kara da cewa rashin albashin da Marigayin yayi ta fama da shi a cikin watanni (9) na bayan da su ka wuce yana cikin abubuwan da su ka jawo rashin lafiyar na sa ya tabarbare ainun har ta kai ga ajali yayi kira.

Takwaran na sa yace ko da yake ya san rai na hannun Ubangiji, amma yana ganin matsalar albashin jihar da ya makale ya kara sababba janyo ajalin wannan Bawan Allah kusa. Ma’aikatan jihar Kogi dai su na cikin wani hali a yanzu.

Shugaban ma’aikatan shari’a na jiha Kogi, Emmanuel Waniko, shi ma ya daura laifin mutuwar Zekery Aguye a kan fama da rashin albashi da ake yi a fadin jihar. Rabon da a biya ma’aikatan albashi tun watan Yulin bara inji Waniko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel