EFCC: Goodluck Jonathan ya bankado sharrin da Gwamnatin Najeriya ta ke yi masa

EFCC: Goodluck Jonathan ya bankado sharrin da Gwamnatin Najeriya ta ke yi masa

Mutanen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun maida martani ga jawabin da mukaddashin shugaban hukumar EFCC yayi a game da irin kudin da aka sata a lokacin Jonathan din yana kan mulki.

Goodluck Jonathan ya iya bada amsa ne ta bakin tsohon Hadimin sa Reno Omokri. Omokri ya ka hankalin gwamnatin shugaba Buhari da ta ji da rahoton da kasar Amurka ta fito da shi kwanan nan game da irin barnar da ake yi a Najeriya.

Kwanan nan ne Amurka ta gano cewa akwai alamar tambaya a game da yaki da satar da wannan gwamnatin Najeriya ta ke yi, don haka Reno Omokri yace Ibrahim Magu ya daina batawa kan sa lokaci wajen yi wa shugaba Jonathan sharri.

KU KARANTA: Mutane 32 su ka sace sama da tiriliyan 1.3 lokacin Jonathan - Ibrahim Magu

Shugaban na EFCC, Magu ya bayyana cewa an sace sama da Tiriliyan 1 a lokacin da Goodluck Jonathan yake mulkin Najeriya. Sai dai Fasto Reno Omokri yace wannan jawabi na EFCC ya nuna gwamnatin Buhari ta na cin karo da kan ta.

Omokri yace a 2016 ne Lai Mohammed yace an yi awon gaba da Tiriliyan 1.3 daga 2006 zuwa 2013, haka kuma bayan nan ne Farfesa Itse Sagaya na PACAC yace gwamnatin Obasanjo da ‘Yaradua da Jonathan ta saci Naira Tiriliyan 1.4 a shekaru 7.

Bayan na kuma shugaban APC watau Adams Oshiomhole taba cewa akwai mutum guda da ya saci Tiriliyan 2.1 a lokacin Jonathan. Reno Omokri yace irin wannan tafka da warwara da APC ke yi ya nuna cewa sam babu gaskiya a lamarin ta.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari da Atiku za su gurfana a gaban Kotu

Tsohon Hadimin Jonathan din yace Amurka dai ta karyata maganar Adams Oshiomhole tuni, ya kuma ce ba yau aka saba jin EFCC da tsula karya ba. Omokri yace alkaluman TI sun nuna cewa an fi samun nasara wajen yaki da sata lokacin Jonathan.

A jawabin na sa, Reno Omokri ya bayyana irin badakalar da aka tafka a kamfanin NNPC kwanaki da kuma yadda aka ji Tinubu yana ikirarin ya fi wata jiha gaba daya arziki da sauran zargin da ke wuyan sa iri-iri yayin da APC ke cewa tana yaki da barayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel