Kisan wani soja a jihar Taraba ya sanya mutane yin hijira zuwa jihar Nasarawa

Kisan wani soja a jihar Taraba ya sanya mutane yin hijira zuwa jihar Nasarawa

- Matsalar rashin tsaro dai a Najeriya, na kwan-gaba kwan-baya

- Wasu mutane da har yanzu ba a da tabbacin sojoji ne ko 'yan ta'adda, sun yi barazanar kone wani gari a cikin jihar Taraba

Wasu mazauna kauyen Shinkai na karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba, sun fa ra guduwa su na barin gidajen su, bayan barazanar da aka yi musu na cewar za a kawowa kauyen na su hari, saboda zargin da ake yi musu na kashe wani jami'in soja.

A bayanin da mai garin yayi Malam Labaran Abdu, ya ce wasu mutane sanye da kaki sun zo kauyen nasu ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, inda suke zargin cewa an kashe musu dan uwansu.

Kashe wani soja a jihar Taraba ya sanya mutane yin hijira zuwa jihar Nasarawa
Kashe wani soja a jihar Taraba ya sanya mutane yin hijira zuwa jihar Nasarawa
Asali: Original

"Mai garin ya fadawa mutanen cewar ba su da masaniya akan lamarin, amma mutanen ba su yadda ba, inda suka yi musu barazanar za su dawo bayan kwana uku su kone garin idan har ba su fito da wanda ya kashe sojan ba."

"Wannan barazanar ce ta sanya mutanen kauyen suke guduwa suna shiga jihar Nasarawa," inji mai garin.

Labaran ya ce kisan da aka yi wa mutumin ya faru ne a can cikin daji, kilomita 15 daga kauyenmu zuwa wurin, amma bai ga dalilin da ya sa mutanen suke so su dora alhakin kisan akan mutanen kauyen Shinkai ba.

KU KARANTA: Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'

A lokacin da ya ke na sa jawabin, Mista Simon Dogari, kwamishinan ya da labarai na jihar ta Taraba, ya ce sun samu rahoton cewa akwai matsala a kauyen Shinkai, bayan rikicin da aka yi tsakanin makiyaya da kuma wasu sojoji da ake tunanin 'yan "Operation Whirl Stroke" ne, rikicin ya sa an kashe daya daga cikin sojojin.

Kwamishinan ya ce shima yana mamakin yanda aka yi sojojin da aka tura su aiki jihar Binuwai, su ke shigowa jihar Taraba.

Ya ce amma zuwa yanzu, an saka shugaban karamar hukumar Wukari, akan ayi bincike kwakkwara akan lamarin. Sannan Kwamishinan ya roki mutanen Shinkai da su kwantar da hankalin su, gwamnati za ta yi iya bakin kokarin ta wurin tabbatar da zaman lafiya a kauyen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel