Ba ni da hannu a rikicin siyasar jihar Kano - Kwankwaso

Ba ni da hannu a rikicin siyasar jihar Kano - Kwankwaso

- A dai-dai lokacin da mutane da yawa suke dora alhakin rikicin zaben jihar Kano akan tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, sai gashi Sanatan ya fito ya na kare kan sa akan rikicin da ya faru

- Sanatan ya ce ba shida hannu ko kadan a rikicin da yake faruwa a jihar ta Kano, sannan ya cigaba da rokon mabiyansa akan su cigaba da zama wakilai na gari

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nesanta kan shi da kuma jam'iyyar PDP, daga rikicin siyasar da ya faru a jihar Kano.

Sanarwar da ta fito daga bakin wata ta hannun daman shi, Binta Spikin, a ranar Talatar nan da ta gabata, ta bayyana cewa jama'a na ya da jita-jitar ne saboda kawai su ba ta wa Sanata Kwankwaso suna.

Ba ni da hannu a rikicin siyasar jihar Kano - Kwankwaso
Ba ni da hannu a rikicin siyasar jihar Kano - Kwankwaso
Asali: Depositphotos

"A lokacin da ya ke gwamnan jihar nan, babban burinsa shine ya ga walwala da jin dadin al'ummar jihar Kano, kuma hakanne ya saka shi ya dinga daukar 'ya'yan talakawa yana fita da su kasashen waje domin karatu."

"Saboda haka ina sanar da jama'a Sanata Kwankwaso bai taba kuma ba zai taba tada tarzoma a jihar Kano ba. Idan ba ku manta ba kwanaki kadan kafin a sake zabe ya fitar da sanarwar cewa mutanen jihar Kano su kwantar da hankalinsu su yi zabe ba tare da tashin hankali ba".

KU KARANTA: Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'

A karshe ta yi kira ga magoya bayan Sanata Kwankwason akan su zama 'yan kasa na gari, saboda hakan ne zai saka sunansu ba zai ba ci ba.

"Sannan Sanata Kwankwaso zai yi amfani da wannan damar wurin yi wa wadanda suka rasa rayukansu a wannan zabe. Sannan ya yi addu'a ga wadanda suka ji ciwo Allah ya ba su lafiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel