Za mu nemi mukaman Majalisar Wakilai da Dattawa – Inji PDP

Za mu nemi mukaman Majalisar Wakilai da Dattawa – Inji PDP

Ana iya samun rikici tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma rinjaye a majalisar tarayya da PDP mai adawa a game da zaben mukaman majalisa da za ayi cikin ‘yan kwanakin nan masu zuwa a Najeriya.

Jam’iyyar PDP tace za ta nemi takarar shugabancin majalisar kasar domin babu wata doka da ta ce dole sai jam’iyyar da ke da rinjaye ce za ta kafa shugabanni a majalisa. Kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana wannan.

Kola Ologbondiyan ya nuna cewa PDP za tayi takarar shugaban majalisar dattawa da mataimakin sa da kuma shugaban majalisar wakilan da kujerar mataimakin sa, a cewar sa dokar kasa ta ba kowa ba tare da duba da jam’iyya ba.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa sun ja-kunnen Ministan Najeriya da ke neman sabon aron kudi

Sakataren yada labaran yayi wannan jawabi ne domin maida martani ga shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, inda ya tuna masa da cewa ‘yan majalisa su na cin gashin kan-su ne ba wai su na zaman wani bane a Najeriya.

APC mai Sanatoci 65 tana kokarin gujewa abin da ya faru a majalisar tarayya a 2015 inda ita kuma PDP tace da ita za ayi takarar mukaman majalisar a wannan karo. A Majalisar Tarayya APC ke da rinjaye da ‘yan majalisa har 211.

Jam’iyyar APC ta zabi Sanata Ahmad Lawan ne domin ya gaje kujerar Bukola Saraki. Sai dai a cikin jam’iyyar ma akwai irin su Sanata Mohammed Ali Ndume wanda yake ganin APC ba tayi daidai na daukar wannan mataki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel