Majalisar Najeriya ta gargadi Minista Sirika game da shirin cin bashi

Majalisar Najeriya ta gargadi Minista Sirika game da shirin cin bashi

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta gargadi Ministan harkokin jiragen sama na kasar nan, Hadi Sirika, a kan sabon shirin da yake yi na aro makudan kudi har dala milyan 461 domin yin wasu aikace-aikace.

‘Yan majalisar sun ce Ministan na da niyyar karbo bashin kudi ne da sunan wasu gyare-gyare da za ayi a filin jiragen saman Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan kwanaki Hadi Sirika ya karbo aron Dala miliyan 500 da nufin za ayi wannan aiki.

Shugaban kwamitin harkokin jiragen sama a majalisa yace ban da wadannan tarin kudi, an warewa ma’aikatar kasar kudi har Naira biliyan 47.5 a cikin kasafin kudin shekarar bana. Shugaban kwamitin harkokin jiragen sama a majalisa.

KU KARANTA: Gwamna ya bada kwangiloli ana saura watanni 2 ya gama mulki

Majalisar Najeriya ta gargadi Minista Sirika game da shirin cin bashi
Ministan harkokin jiragen sama a Najeriya Hadi Sirika
Asali: Facebook

‘Yar majalisar APC Nkeiruka Onyejeocha na yankin jihar Abia, ta bayyana a wajen wani zama da aka yi a majalisar game da kasafin kudin Najeriya. Nkeiruka Onyejeocha ke cewa kashi 11% na kasafin bara kurum ma’aikatar da dabakka.

‘Dan majalisar Kano, Honarabul Bashir Babale wanda shi ne shugaban wannan kwamiti a Majalisar, shi ma ya bayyana cewa tsarin kasafin kudin da ake amfani da shi ba zai kai kasar ko ina ba a wannan tafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel