'Yan bindiga sun sace dan asalin kasar Koriya ta Arewa a Zamfara

'Yan bindiga sun sace dan asalin kasar Koriya ta Arewa a Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun sace wani likita, Mista Jeng Sunail, dan asalin kasar Koriya ta Arewa da ke aiki da babban asibitin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ce ta sanar da hakan a cikin wani jawabi da kakakin ta, DSP Shehu Mohammed, ya fitar.

A cewar jawabin, abokin aikin likitan ne mai suna Dakta Li Dung ya sanar da rundunar 'yan sanda labarin sace likitan ta hannun ofishinta da ke karamar hukumar Tsafe.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa majiyar mu cewar wasu 'yan bindiga ne suka kutsa rukunin gidajen ma'aikatan asibitin da misalin karfe 9:00 na daren ranar Litinin inda su ka wuce kai tsaye zuwa gidan Sunail tare da yin awon gaba da shi zuwa wurin da babu wanda ya sani.

'Yan bindiga sun sace dan asalin kasar Koriya ta Arewa a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Yari
Asali: Depositphotos

Sai dai tawagar jami'an 'yan sanda da su ka isa gidan likitan bayan samun rahoto, sun ce sun samu kofar gidan a bude ba tare da alamar an balle ta ko an shiga gidan ta karfin tsiya ba.

DUBA WANNAN: Ma'aikata sun bawa FG shawarar yadda za ta samu kudin biyan sabon karin albashi

Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Celestine Okoye, ya bawa jami'an 'yan sandan na sashen binciken aiyukan ta'addanci (CID) da na binciken sirri (SIB) da rundunar yaki da garkuwa da mutane umarnin fara gudanar da bincike tare da fara kokarin kubutar da Dakta Sunail.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel