A karshe: Gwamnan jihar Bauchi ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa ya fadi zabe

A karshe: Gwamnan jihar Bauchi ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa ya fadi zabe

- Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana wa duniya dalilin da ya sa ya fadi zaben gwamnan jihar da aka gudanar

- A zantawarsa da manema labarai a Abuja, gwamna Abubakar ya ce Allah ne kadai ya barwa kansa sanin dalilin da ya sa ya fadi zaben

- Gwamnan ya ce tuni ya taya wanda ya lashe zaben murna, kuma ya bukaci ya ja hankalin magoya bayansa da kada a tayar da hankalin jama'a

Dan takarar gwamnan jihar Bauchi karkashin jam'iyyar APC kuma Gwamnan jihar mai ci a yanzu, Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana wa duniya dalilin da ya sa ya fadi zaben gwamnan jihar da aka gudanar makwannin da suka gaba.

A zantawarsa da BBC a Abuja ranar Talata, gwamna Abubakar ya ce Allah ne kadai ya barwa kansa sanin dalilin da ya sa ya fadi zaben.

Sai dai ya ce yana da tabbacin cewa shi ne ya ci zabe a duka kananan hukumomin jihar, "idan ban da kananan hukumomi guda biyu wadanda aka yi aringizon kuri'u," a cewarsa.

"Don haka sakamakon zaben ba ya nuni da cewa al'ummar jihar ba sa sonmu, don mun yi abin so. Idan aka shiga lungu da sako, za a ga wani aiki da gwamnatin APC ta yi," in ji shi.

KARANTA WANNAN: Dan takarar gwamnan Yobe a PDP ya ce ba zai kalubalanci nasarar APC a kotu ba

A karshe: Gwamnan jihar Bauchi ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa ya fadi zabe
A karshe: Gwamnan jihar Bauchi ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa ya fadi zabe
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya ce tuni ya taya wanda ya lashe zaben murna, kuma ya bukaci ya ja hankalin magoya bayansa yayin da suke murnar cin zabe domin "kada a tayar da hankalin jama'a."

Haka zalika, Mr Abubakar ya ce ya ji dadin yadda aka gudanar da zabuka a jihar ba tare da an samu tashin tashina ko zubar da jinin jama'a ba.

"Allah ne ke ba da mulki ga wanda yake so, kuma shi ne mai karba daga hannun wanda yake so, a lokacin da yake so," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa wannan ne dalilin da ya sa ya taya abokin hamayyarsa murnar samun nasara.

Hakazalika ya ce shi ba zai kalubalance sakamakon ba a gaban kotu, sai dai ya ce jam'iyyarsa tana da hakkin kalubalantarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel