Ma'aikata sun bawa FG shawarar yadda za ta samu kudin biyan sabon karin albashi

Ma'aikata sun bawa FG shawarar yadda za ta samu kudin biyan sabon karin albashi

Wani bangare na ma'ikatan gwnamnati a jihar Enugu sun bawa gwamnatin tarayya shawarar cewar ta rage kudin gudanar da harkokin gwamnati da wadanda masu rike da mukaman siyasa ke warewa domin tsaro domin samun sukunin biyan sabon karin albashi.

Ma'aikatan sun bayar da shawarar ne a Enugu yayin gana wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) inda suke bayyana dalilin da yasa gwamnatin jihohi suka gaza biyan ma fi karancin albashi na N18,000.

Ma'aikata sun bawa FG shawarar yadda za ta samu kudin biyan sabon karin albashi
Ma'aikata sun bawa FG shawarar yadda za ta samu kudin biyan sabon karin albashi
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

Da yawan ma'aikatan sun bayyana cewar matukar gwamnatocin jihohi zasu rage yawan kudaden da suke kashe wa ta wasu hanyoyin badangarci, tabbas biyan sabon karin albashin ba zai yi masu wuya ba.

Wata masaniyar shari'a, uwargida Nkechi Afadigwe, ta bukaci shugaba Buhari da ya amince da biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi kamar yadda majalisa ta yi.

"Idan ma'aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban zasu rage adadin kudadensu na gudanarwa, biyan sabon karin albashin ba zai zama wani abun wahala ba," a cewar Afadigwe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel