Ajimobi ya bada kwangilolin Biliyan 30 yana daf da barin ofis – Makinde

Ajimobi ya bada kwangilolin Biliyan 30 yana daf da barin ofis – Makinde

Seyi Makinde wanda ya lashe zaben jihar Oyo a karkashin jam’iyyar PDP mai adawa ya fara korafi game da makudan kwangilolin da gwamna mai-ci a jihar watau Abiola Ajimobi, ya bada kwanan nan.

Mista Makinde mai shirin darewa a kan mulkin jihar Oyo a karshen Watan Mayu ya bayyana cewa gwamna Abiola Ajimobi ya bada kwangila har na Biliyan 30 a taron majalisar zartarwa na jihar Oyo da aka yi na makon jiya.

Gwamnan mai jiran gado yayi wannan jawabi ne ta bakin Hadimin sa na kafafen yada labarai, Prince Dotun Oyelade. Mista Dotun Oyelade yake cewa gwamnan yana ta garajen bada kwangiloli kafin wa’adin sa ya cika a watan jibi.

Makinde yake cewa akwai alamar tambaya game da wannan mataki da gwamnatin jihar Oyo ta dauka na fitar da sababbin kwangiloli alhali kusan watanni 2 kacal su ka ragewa Sanata Abiola Ajimobi a kan karagar gwamna a Oyo.

KU KARANTA: Amai da gudawa ya kama mutanen Ajimobi a sanadiyyar abincin taro

Ajimobi ya bada kwangilolin Biliyan 30 yana daf da barin ofis – Makinde
Gwamna Abiola Ajimobi ya fitar da kwangiloli daf da cikar wa'adin sa
Asali: Depositphotos

Zababben gwamnan jihar yake cewa akwai tarin bashin da ke kan gwamnatin Oyo tun 2011 don haka yake ganin bai dace a kirkiri a wasu ayyuka a daidai wannan lokaci ba, inda yace da ana neman kwalwale kudin jihar ne.

Haka kuma ‘dan takaran na APC da yayi nasara a zaben gwamnan yace an shirya sakin wadannan kudi tuni da wasu ma’aikata da sunan za su duba ayyukan. Hadimin sabon gwamnan yake cewa ma’aikatan jihar za su kuka da kan su.

Bayan wannan kuma, jawabin Prince Dotun Oyelade ya nuna cewa ana shirin karawa ma’aikatan makarantun gaba da sakandare albashi wanda a karshe shi zai yi kashin wadannan kudi idan ya hau mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel