Kotu na gab da sakin Maryam Sanda, Lauya ya ce babu kwakwarin hujjan da aka gabatar

Kotu na gab da sakin Maryam Sanda, Lauya ya ce babu kwakwarin hujjan da aka gabatar

- Babu laifin da na aikata, Maryam ta laburtawa kotu

- Idan lauyan gwamnati bai kawo wani hujja ba, za'a wanketa

Maryam Sanda, matar da ake zargi da kisan maigidanta, Bilyaminu Bello, ta bayyanawa kotu cewa babu laifin da ta aikata kan tuhumar da ake mata.

An gurfanar da ita tare da dan uwanta Aliyu Sanda; mahaifiyarta, Maimuna Aliyu da mai aikinsu, Sadiya Aminu, wadanda aka yiwa zargin taimakawa wajen boye hujja ta hanyar goge jinin mamacin.

Yayinda aka koma shari'ar Maryam ranar Talata, Lauyanta Olusegun Jolaawo, ya bayyanawa kotu cewa lauyoyin gwamnati basu kawo kwararan hujjojin da zai bukaci ta kare kanta ba.

Ya kara da cewa duk hujjojin da lauyoyin gwamnati suka kawo an rigaya da watsi da su lokacin da shaidu ke gabatar da shaidunsu.

KU KARANTA: Idan aka sake zabe sau goma, Atiku zai fadi sau gomA

Saboda haka, kotu ta wanke Maryam Sanda daga zargin kisan kai.

Hakazalika, lauyan mahaifiyar Maryam da dan uwanta ya bukaci kotu ta sakesu saboda lauyoyin gwamnati basu kawo kwararan hujjojin da zai bukacesu su kare kansu ba. Amma lauyan gwamnati, Fidelis Ogbobe, ya yi kirag kotun tayi watsu da wannan bukata da lauyan Maryam keyi.

Alkalin kotu, Jastis Yusuf Halilu, ya daga zaman zuwa ranar 4 ga watan Afrilu, 2019. Idan alkalin ya amsu bukatar lauyoyin dake kare wadanda ake zargi da laifi, za'a sakesu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel