Ta leko za ta bare: INEC ta dakatar bayar shaidar cin zabe ga 'yan takarar APC a Zamfara

Ta leko za ta bare: INEC ta dakatar bayar shaidar cin zabe ga 'yan takarar APC a Zamfara

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta ce ta dakatar da bayar da shaidar samun nasarar lashe zabe ga 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar Zamfara bayan samun takardar hukuncin da kotu ta yanke a kan zaben fidda 'yan takarar jihar da APC ta gudanar.

INEC ta bayyana cewar dakatar da mika shaidar cin zabe ya biyo bayan aike ma ta da kwafin hukuncin kotu da aka yi a yau, Talata, 26 ga watan Maris.

A ranar Laraba, 27 ga watan Maris, ne INEC ke shirin mika takaradar shaidar ga 'yan takarar APC da su ka samu nasara a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

'Yan takarar da wannan hukunci ya shafa sun hada da dan takarar gwamnan mambobin majalisar dokokin jihar da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

A baya Legit.ng ta sanar da ku cewar kotun daukaka kara da ke zaman ta a Sokoto, karkashin jagorancin Justis Tom Yakubu, ta jingine hukuncin wata babbar kotun Zamfara akan zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ta leko za ta bare: INEC ta dakatar bayar shaidar cin zabe ga 'yan takarar APC a Zamfara
Gwamnan Zamfara da jiga-jigan 'ya'yan APC a jihar
Asali: Facebook

Lamarin ya shafi samar da dan takarar gwamna da kuma yan takarar majalisun dokokin jiha da na kasa, kamar yadda NAN ta ruwaito.

Wanda ya shigar da karar, Sanata mai wakiltan Zamfara ta Tsakiya, Kabiru Marafa ya sake jadada cewa bai dace a bar jam'iyyarsa ta APC ta tsayar da 'yan takara ba a zaben da za a gudanar a watan Fabrairu da Maris na wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Bangarorin gwamnati 5 da su ka yi kaurin suna wajen cin hanci - Binciken SERAP

Marafa ya ce Hukumar zabe mai zaman kanta ta yi biyayya da umurnin babban kotun Abuja inda ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta APC ba za ta fitar da 'yan takara ba.

Sanatan wanda kuma shine Ciyaman din kwamitin majalisar dattawa a kan albarkatun man fetur ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi da menema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

Ya ce INEC ta tsaya a kan bakan ta na haramtawa jam'iyyar APC reshen Zamfara fitar da 'yan takara saboda gaza gudanar da zaben fidda gwani a cikin lokacin da aka kayyade mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel