Ifeanyi Ubah ya karyata batun sauya sheka zuwa APC

Ifeanyi Ubah ya karyata batun sauya sheka zuwa APC

Ifeanyi Ubah, zababben sanata mai wakiltan yankin kudancn Anambra,ya yi martani ga rahotannin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kafafen watsa labarai da dama sun rahoto cewa sanatan wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar Young People’s Party (YPP) ya sauya sheka zuwa APC a daren ranar Litinin, 25 ga watan Maris.

Da yake hira tare da jaridar Premium Times a yammacin ranar Talata, 26 ga watan Maris, Mista Ubah yace yana tattaunawa ne da APC, amma bai koma jam’iyyar ba.

Ifeanyi Ubah ya karyata batun sauya sheka zuwa APC
Ifeanyi Ubah ya karyata batun sauya sheka zuwa APC
Asali: Depositphotos

“Har yanzu ina tare da jam’iyyar YPP, babu rikici a jam’iyyarmu toh me zai sani barin jam’iyyar? Koda dai Shugaban APC ya gabatar dani a matsayin sanatan APC mai zuwa a taron cin abincin dare da na halarta, amma ba sabon abu bane don Shugabannin jam’iyyu sunyi haka,” inji shi.

Mistah Ubah yace yana da shari’a a kotu da ke kalubalantar sakamakon zabe yayinda ya bayyana cewa har yanzu shi dan YPP ne.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, bayan lashe zaben sanata mai wakiltan kudancin Anambra a jam’iyyar Young Peoples Party (YPP), Ifeanyi Ubah ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Ba mu yarda ba: APC tayi watsi da ranar da INEC ta tsayar don gudanar da zabe a Adamawa

Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan ya musanta rahotannin cewa yana shirin sauya sheka.

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana komawar Ubah zuwa jam’iyya mai mulki a wani taron tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da sanatocin APC a fadar shugaban kasa a daren ranar Litinin, 26 ga watan Maris.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel