Rugujewar gidaje: Buhari ya gargadi masu yin gine gine ba bisa ka'ida ba

Rugujewar gidaje: Buhari ya gargadi masu yin gine gine ba bisa ka'ida ba

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu gina gidaje ba bisa ka'ida ba wanda har ya ke haddasa rugujewar gidaje a fadin kasar

- Buhari ya ce duk wanda aka kama zai dandana kudarsa a kotun shari'a

- Ya ce bai kamata ace rayuka su ci gaba da salwanta saboda son zuciya da rashin bin dokoki ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu gina gidaje ba bisa ka'ida ba wanda har ya ke haddasa rugujewar gidaje a fadin kasar, yana mai cewa duk wanda aka kama zai dandana kudarsa a kotun shari'a.

Ya yi wannan gargadin a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabannin kungiyar kwararru kan ilimin kididdiga da darajta kayan gida ta kasa (NIQS) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewar sa, rushewar gine gine da ke ta faruwa a wasu sassa na kasar ya faru ne sakamakon rashin bin ka'idoji da kuma yin ingantattun gine gine.

KARANTA WANNAN: Daga INEC: Sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi zagaye na biyu

Rugujewar gidaje: Buhari ya gargadi masu yin gine gine ba bisa ka'ida ba
Rugujewar gidaje: Buhari ya gargadi masu yin gine gine ba bisa ka'ida ba
Asali: Twitter

Ya ce, "Da wannan, rushewar gine gine a Legas da wasu sassa na kasar, akwai bukatar daukar mataki na ganin cewa ana gine gine masu inganci da kuma bin ka'idoji idan har aka zo maganar gine gine a kasar.

"Bai kamata ace rayuka su ci gaba da salwanta saboda son zuciya da rashin bin dokoki ba. Maganar gaskiya guda daya, babu dalilin dora harsashin gini a muhallin da ya sabawa tsarin gini na kasa.

Ina so na baku tabbacin cewa duk wadanda suke da hannu a rugujewar gine gine a kasar za su dandana kudarsu a gaban shari'a," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel