Bangarorin gwamnati 5 da su ka yi kaurin suna wajen cin hanci - Binciken SERAP

Bangarorin gwamnati 5 da su ka yi kaurin suna wajen cin hanci - Binciken SERAP

- Wani bincike da kungiyar SERAP ta gudanar ya bayyana cewar rundunar 'yan sanda ta fi kowacce hukuma kaurin suna wajen cin hanci

- Sakamakon binciken SERAP ya gano cewar 'yan sanda na karbar cin hanci a kaso 54% cikin 100% na mu'amala da su

- Bangaren wutar lantarki ne ya zo na biyu a jerin sahun hukumomin da cin hanci ya yiwa katutu

A wani sabon rahoton sakamakon bincike da kungiyar SERAP mai yaki da cin hanci da tabbatar da gaskiya ta fitar, an gano wasu hukumomi da ma'aikatu biyar da suka yi kaurin suna wajen karbar nagoro a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Rundunar 'yan sanda ce ta zo a mataki na farko yayin da bangaren wutar lantarki ya zo na biyu a jerin hukumomi da ma'aikatu da cin hanci ya yiwa katutu.

Bangarorin gwamnati 5 da su ka yi kaurin suna wajen cin hanci - Binciken SERAP
'Yan sandan Najeriya
Asali: UGC

Ragowar ma'aikatu da aka gano akwai cin hanci da mizanin sa ya kai kaso 70% su ne; bangaren lafiya, shari'a da ilimi. Rahoton ya bayyana cewar ba a samu canji ta fuskar karbar cin hanci a cikin wadannan hukumomi ba a cikin shekaru biyar.

SERAP ta gabatar da sakamakon binciken da ta gudanar mai taken 'Nigeria: Corruption Perception Survey' a otal din sheraton da ke Legas a yau, 26 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

Sakamakon binciken na SERAP ya nuna cewar 'yan sanda na karbar cin hanci a kaso 54% cikin 100% na mu'amala da su, mizanin karbar cin hanci a bangaren wutar lantarki ya kai kaso 49%, kaso 27% a bangaren shari'a, kaso 25% a bangaren ilimi da kaso 20% a bangaren lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel