Ba mu yarda ba: APC tayi watsi da ranar da INEC ta tsayar don gudanar da zabe a Adamawa

Ba mu yarda ba: APC tayi watsi da ranar da INEC ta tsayar don gudanar da zabe a Adamawa

Jam'iyyar Progressives Congress (APC) reshen jihar Adamawa ta ce ba ta amince da tsayar da ranar 28 ga watan Maris ba da INEC tayi a matsayin ranar da za ayi zaben gwamna na cike gurbi a jihar.

Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar, Alhaji Ahmed Lawal ne ya bayar da sanarwar a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ranar Talata a garin Yola kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lawal ya ce INEC ba ta tuntubi jam'iyyar su ba kafin ta tsayar da sabon ranar da za a gudanar da zaben.

Ya yi ikirarin cewa a baya sun ji kishin-kishin cewa za a gudanar da zaben ne a ranar Alhamis 28 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

Zaben Adamawa: APC tayi watsi da sabon ranar zabe da INEC ta tsayar
Zaben Adamawa: APC tayi watsi da sabon ranar zabe da INEC ta tsayar
Asali: UGC

"INEC ba ta tuntubi jam'iyyun siyasar da za su fafata a zaben ba kafin ta tsayar da sabon ranar zaben ciki gibin.

"Muna zargin akwai kullaliya saboda mun ji kishin-kishin cewar za a sake zaben a ranar Alhamis 28 ga watan Maris kuma daga baya hakan ya zamo gaskiya.

"Ba mu tsoron maimaita zaben amma ya dace INEC tayi abinda ya kamata.

"Ta yaya za ka saka zabe a ranar aiki. Shin ba a so ma'aikatan gwamnati suyi zaben ne.

"Za mu gabatar da korafin mu a kan lamarin ga INEC," inji shi.

NAN ta ruwaito cewa babban kotun da ke zamanta a Yola ta janye umurnin da ta bayar da hana INEC gudanar da zaben ciki gibin a jihar Adamawa.

Saboda haka INEC ta tsayar da ranar 28 ga watan Maris domin gudanar da zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel