Zaben raba gardama a Kano babban abin kunya ne ga dimokradiyya - CSO

Zaben raba gardama a Kano babban abin kunya ne ga dimokradiyya - CSO

Kungiyar kare hakkin farar hula na Kano wato Kano Civil Society Forum ta soki zaben rabar gardama da aka gudanar a jihar kwana-kwanan nan inda ta ce an tafka gidadanci da abin kunya ga demokradiyar Najeriya.

A sakon da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta da sakataren ta, Kwamared Ibrahim A. Waya da Peter Hassan Tijjani, tayi ikirarin cewa anyi rikici sosai tare da razana masu zabe da kashe-kashe.

A cewar kungiyar, "Demokradiyar Najeriya yana sauyawa zuwa siyasar zalunci inda shugabani ke amfani da amfani da karfi da razana al'umma suka zama hanyoyin da ake amfani da su wurin samun mulki a maimakon kuri'u.

Zaben raba gardama a Kano babban abin kunya ne ga dimokradiyya - CSO
Zaben raba gardama a Kano babban abin kunya ne ga dimokradiyya - CSO
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

"A matayin mu na kungiyar kare hakkin farar hula, abinda muka lura da shi a wasu rumfunan zabe ya yi kama da yaki ne tsakanin abokan gaba biyu ba zabe tsakanin jam'iyyun siyasa biyu da akayi bisa dokoki ba.

Kungiyar kare hakkin farar hular ta zargi Hukumar Zabe INEC da Rundunar 'yan sanda ta fifita bangare guda a zaben inda ta bukaci Sufeta Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya kafa kwamitin bincike a domin gano irin rawar da suka taka a zaben.

"Abinda muka lura da shi a zaben cike gibi na gwamna a jihar Kano shine magudi aka tafka kuma hakan babban abin kunya ce ga demokradiyar Najeriya baki daya.

"Mun lura cewa zaben na ciki gibi na jihar Kano da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris itace zabe mafi muni. An dauko hayar 'yan daban siyasa domin su razana masu zabe su kuma tayar da hankulin al'ummar Kano a kusa dukkan rumfunan zabe. Bai dace mu amince da hakan ba," inji kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel