Sake zabe: Gwamnati tayi magana akan rikici a Kano

Sake zabe: Gwamnati tayi magana akan rikici a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa sabanin rade-radin da ake yi, babu wani rikici a jihar, biyo bayan sanar da sakamakon zaben da aka kammala wanda Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi nasara.

Da yake jawabi ga manema labarai a yau Talata, 26 ga watan Maris, kwamishinan bayanai na jihar, Malam Muhammad Garba yace jihar na cike da zaman lafiya yayinda mutane ke gudanar da harkokin gabansu.

Garba yace gwamnatin Ganduje na yin duk abunda ya kamata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, cewa gwamnati za ta ci gaba da wanzar da zaman lafiya da aminci a jihar.

Sake zabe: Gwamnati tayi magana akan rikici a Kano
Sake zabe: Gwamnati tayi magana akan rikici a Kano
Asali: Depositphotos

Kwamishinan ya kuma karyata zargin rasa rayuka a lokacin sake zabe, inda ya bayyana cewa “a lokacin da PDP tayi ikirarin cewa an rasa rayuka byu a karamar hukumar Nasarawa a lokacin zabe, mun je yankin da asibitoci domin bincike, amma ku yarda dan, bamu ga tabbass a ikirarin ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kasafin kudin 2019 ya hadu da cikas yayinda Udoma, Ahmad da sauransu suka kaurace wa majalisa

“Don haka, na karyata ikirarin sannan na kalubalanci duk wanda ke da bayani akan rasa rayukan a lokacin zaben da ya gabatar da shi. Muna bukatar irin wannan bayani domin mu samu damar bincikar lamarin.”

Garba ya kuma karyata ikirarin cewa babu wani zanga-zangar lumana da wasu matasa suke shirya domin nuna fushi ga sanar da sakamakon zaben da INEC tayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel