Shugabancin majalisa: Ban amince da tsarin jam'iyya ba - Sanata Ndume

Shugabancin majalisa: Ban amince da tsarin jam'iyya ba - Sanata Ndume

Sanata mai wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu, Ali Ndume, bai amince da shawarar jam'iyyar APC na cewar jagoran majalisa, Sanata Ahmed Lawan, ya zama shugaban majalisar dattijai ba.

Kwamitin jam'iyyar APC karkashin shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole, ne ya gabatar da Lawan ga shugaba Buhari a matsayin wanda APC ke son ya zama sabon shugaban majalisar dattijai ta 9. Kwamitin ya gabatar da Lawan a daren ranar Litinin yayin wata ganawa da shugaba Buhari.

Ndume, tsohon jagoran majalisar dattijai, ya shaida wa manema labarai a Abuja cewar ba a yi abinda ya dace ba kafin yanke shawarar da APC ta yi.

Shugabancin majalisa: Ban amince da tsarin jam'iyya ba - Sanata Ndume
Sanata Ndume
Asali: Depositphotos

Ya ce ba a tuntubi sanatocin da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar APC ba kafin a yanke shawarar, sannan ya kara da cewa ma fi rinjayen sanatocin jam'iyyar APC basa farin ciki da matakin jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Kwamitin kamfen din Buhari sun kai karar PDP wurin rundunar 'yan sanda da DSS

Sanatan ya ce shawarar da jam'iyya ta yanke ba ita ce abinda shugaba Buhari ke so ba.

Ndume ya bayyana cewar sai da ya sanar da shugaba Buhari da jagotran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, kudirinsa na son yin takarar shugabancin majalisa, kuma dukkan su sun sahale ma sa ya nemi kujerar shugaban majalisar dattijai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel