Yanzu Yanzu: INEC ta sanya 28 ga watan Maris don sake zabe a Adamawa

Yanzu Yanzu: INEC ta sanya 28 ga watan Maris don sake zabe a Adamawa

- Hukumar zabe mai zaman kanta, ta sanya ranar 28 ga watan Maris domin sake zaben gwamna a jihar Adamawa

- A safiyar yau Talata ne dai wata babbar kotun Adamawa ta dage umurnn da ya hana INEC gudanar da zabe a ranar Asabar, 23 ga watan Maris

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta sanya ranar 28 ga watan Maris domin sake zaben gwamna a jihar Adamawa.

Babbar kotun Adamawa, a ranar Talata, 26 ga watan Maris, ta ba INEC umurnin ci gaba da shirin gudanar da zabe a jihar.

Yanzu Yanzu: INEC ta sanya 28 ga watan Maris don sake zabe a Adamawa
Yanzu Yanzu: INEC ta sanya 28 ga watan Maris don sake zabe a Adamawa
Asali: Original

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, wata babbar kotun Adamawa da ke da zama a Yola ta dage wani umurni da ya hana sake zaben gwamna yiwuwa a jihar. Kotun ta dage umurnin ne biyo bayan rashin gudanar da zabe a mazabu 44 da ke jihar.

Yayinda aka gudanar da zabe a sauran jihohi a ranar Asabar, 23 da watan Maris, ba a gudanar da zabe ba a Adamawa sakamakon karar da dan takarargwamna a jam’iyyar Movement for Restoration and Defence for Democracy (MRDD), Mustafa Shaba, ya shigar akan hukumar zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kasafin kudin 2019 ya hadu da cikas yayinda Udoma, Ahmad da sauransu suka kaurace wa majalisa

Shaba ya maka hukumar zabe a kotu kan cire logon jam’iyyarsa a kayayyakin zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel