Yanzu Yanzu: Kasafin kudin 2019 ya hadu da cikas yayinda Udoma, Ahmad da sauransu suka kaurace wa majalisa

Yanzu Yanzu: Kasafin kudin 2019 ya hadu da cikas yayinda Udoma, Ahmad da sauransu suka kaurace wa majalisa

Kasafin kudin 2019, a ranar Talata, 26 ga watan Maris ya hadu da babban cikas yayinda shugabannin ma’aikatun gwamnatin tarayya suka kauracewa wata gayyatar da kwamitin hadin gwiwa na majalisa akan kasafin kudi, kudi, tallafi, basussuka da sauransu tayi masu.

Shugabannin ma’aikatun da abun ya shafa sun hada da, Ministan tsare-tsare na kasa, Udo Udoma, Ministar kudi, Aisha Ahmad; manajan darakta na kamfanin man fetur din Najeriya, Maikanti Baru, da sauransu.

An kafa kwamitin na hadin gwiwa ne domin nazari akan yadda shugabannin ma’aikatun na gwamnati suka tafiyar da kasafin kudin 2018, wanda shine sigar da za a bi wajen aiwatar da kasafin kudin 2019.

Yanzu Yanzu: Kasafin kudin 2019 ya hadu da cikas yayinda Udoma, Ahmad da sauransu suka kaurace wa majalisa
Yanzu Yanzu: Kasafin kudin 2019 ya hadu da cikas yayinda Udoma, Ahmad da sauransu suka kaurace wa majalisa
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai bayan dage zaman, Shugaban kwamitin na hadin gwiwa kuma Shugaban majalisar wakilai akan kudi, Babangida Ibrahim, yace kalubalan shine cewa za a samu jinkiri a kasafin kudin 2019.

A halin da ake ciki, ba a sanya sabon ranar sauraron lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta sanya 28 ga watan Maris don sake zabe a Adamawa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) a ranar Litinin, 26 ga watan Maris ta jinjina wa manufofn Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tattalin arziki.

Jam’iyyar tace yan Najeriya zasu fara more ingantacciyar tattalin arziki da wannan kyakyawar manufa na Shugaban kasar.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban jam’iyyar APGA, Victor Oye, yace yan Najeriya su bada goyon bayan su da addu’o’i ga shugaban kasar, inda ya kara da cewa Buhari na bukatan shekaru takwas kamar yanda kundin tsari ta tanadar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel