Jama'ar Bauchi sun yi watsi da kai saboda rashin cika alkawari - Kauran Bauchi ya caccaki Mohammmad Abubakar

Jama'ar Bauchi sun yi watsi da kai saboda rashin cika alkawari - Kauran Bauchi ya caccaki Mohammmad Abubakar

Zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammad, ya bayyana cewa mutajama'ar jihar sun yi watsi da gwamnan jihar, Mohammad Abubakar, ne saboda saba alkawuran da yayi lokacin da yake yakin neman zabe.

Bala Mohammed, wanda yayi takara karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya samu kuri'u 515,113 yayinda Mohammad Abubakar ya samu kuri'u 500,625 a zaben.

A jawabin da ya gabatar, Bala Mohammed yace mutanen Bauchi sunyi zaton cewa lokacin da suka zabi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a 2015, za su samu sauyin rayuwa amma akasin aka suka gani.

Yace: "Shekaru hudu da suka shude, mutanen jihar Bauchi sun zabi wata gwamnatin da suke tunanin za ta kawo musu sabon rayuwa."

"Amma wannan gwamnatin ta gaza cika alkawuranta da ta yiwa a lokacin yakin neman zabe kuma ahakan yasa suka ki zabenta."

"Saboda haka kunyi zabi ta akwatin zabe na rashin barin rana goben jiharmu hannun wadanda basu da hangen nesa da ikon kawo canjin da muke bukata."

KU KARANTA: Jam'iyyun siyasa 42 sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben Kano

Ya karashe da cewa gwamnatinsa za ta hada kai da gwamnati mai shudewa wajen kawo cigaban jihar.

A jihar Kano kuma, Jam'iyyun siyasa arba'in da biyu a jihar Kano karkashin kungiyar jam'iyyar adawa CUPP sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamnan ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019 da aka gudanar.

Sun yi zargin cewa an tafka magudi da rashin gaskiya a zaben.

Shugaban kungiyar CUPP na jihar, Mohammed Abdullahi-Rahi, ya bayyana matsayar kungiyar a wata da manema labarai a jihar Kano ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel