Wani babban dan kashenin Buhari ya isa Kebbi daga Abuja a kafa

Wani babban dan kashenin Buhari ya isa Kebbi daga Abuja a kafa

Wani mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sani Ahmed wanda ya fara tafiya daga Abuja kimanin makonni biyu da suka gabata, ya isa Birnin Kebbi a yankin Kalgo da ke jihar.

Sani, wanda ya samu tarba daga matarsa da diyarsa Sa’adatu da Aisha suka, da magoya bayan APC da sauran masoya a filin wasan Haliru Abdul dake Birnin Kebbi, sun ce zai zarce gidan gwamnati don gabatar da wasika ga gwamna Abubakar Atiku Bagudu.

Yace “ina murna da yanda diyata da matata Sa’adatu da Aisha suka tarbe ni.

“Masha Allah, na isa Birnin Kebbi ina a hanyar Gidan Gwamnati”.

Babban dan kashenin Buhari ya isa Kebbi a kafa daga Abuja
Babban dan kashenin Buhari ya isa Kebbi a kafa daga Abuja
Asali: Facebook

Ya soma tafiya ne daga Abuja makonni biyu da suka gabata. bisa murnar nasara da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran yan takaran Jam’iyyar APC suka samu a zaben kasa.

KU KARANTA KUMA: Jihar Bauchi ba za ta sake goya wa azzalumi baya ba — Dogara

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyun siyasa arba'in da biyu a jihar Kano karkashin kungiyar jam'iyyar adawa CUPP sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamnan ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019 da aka gudanar.

Sun yi zargin cewa an tafka magudi da rashin gaskiya a zaben.

Shugaban kungiyar CUPP na jihar, Mohammed Abdullahi-Rahi, ya bayyana matsayar kungiyar a wata da manema labarai a jihar Kano ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel