Jam'iyyun siyasa 42 sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben Kano

Jam'iyyun siyasa 42 sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben Kano

Jam'iyyun siyasa arba'in da biyu a jihar Kano karkashin kungiyar jam'iyyar adawa CUPP sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamnan ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019 da aka gudanar.

Sun yi zargin cewa an tafka magudi da rashin gaskiya a zaben.

Shugaban kungiyar CUPP na jihar, Mohammed Abdullahi-Rahi, ya bayyana matsayar kungiyar a wata da manema labarai a jihar Kano ranar Talata.

Ya yi zargin cewa zaben zagaye na biyu da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta gudanar cike yake da magudi, rikice-rikice, yiwa jama'a barazana da hana mutane kada kuri'arsu.

KU KARANTA: Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

Game da cewarsa, ta'ddanci da barazana ya faru a yawancin rumfunan zaben da akayi zabe ranar Asabar, inda akayi asarar rayuka, akayi siya-siyan kuri'u da wasu ayyukan da ya sabawa dokar zabe.

Yace: "Ya bayyana karara cewa irin rikice-rikicen da ya faru ranar ga watan Maris da ya kai ga soke zabubbukan wasu rumfunan zabe, bai kai yawan abinda ya faru ranar 23 ga watan Maris ba, amma duk da haka hukumar zabe tayi murus, ta sanar da sakamakon zaben."

"Saboda haka, muna nuna rashin amincewarsu da sanar da Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin zababben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 23 ga Maris."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel