Kotu ta caji wani mutum N150,000, saboda ya saci burodi

Kotu ta caji wani mutum N150,000, saboda ya saci burodi

- Hakika rashin aikin yi yana daya daga cikin kalubalen da kasar nan ke fuskanta, hakan ne ma yasa zaka ji matsaloli na sace-sace yayi yawa a sassa da yawa na kasar nan

- A jiya ne aka gurfanar da wani mutum a jihar Lagos da laifin sata a wani shago

A ranar Litinin, 25 ga watan Maris aka gurfanar da wani mutum mai suna Lukman Babatunde, mai shekaru 62, a gaban alkalin kotun majistire dake unguwar Yaba cikin jihar Lagos, da laifin satar burodi da sabulu a wani shago.

Babatunde wanda yake zaune a cikin jihar ta Lagos, kotu na tuhumarsa da laifin sata. Sannan shima baiyi musu akan tuhumar da ake yi masa ba.

Kotu ta caji wani mutum N150,000, saboda ya saci burodi
Kotu ta caji wani mutum N150,000, saboda ya saci burodi
Asali: Twitter

Mai kawo karar, Sergeant Modupe Olaluwoye, ta bayyanawa kotu cewa mai laifin ya aikata laifin ranar 16 ga watan Mayu da misalin karfe 4 na yamma, a wani babban shago mai suna Trolleys, dake unguwar Yaba, cikin jihar ta Lagos.

A cewarta, wanda ake zargin yaje ya shiga shagon da siffar wanda yaje sayan kaya, inda ya saci kwalaben giya guda hudu, wanda kudinsu ya kai kimanin N31,200.

Sannan ta kara da cewa, bai tsaya a nan ba, sai da ya saci sinkin sabulu mai suna Dettol, shima kudin shi ya kai N3,000, sannan ya dauki man wanke baki guda shida, kudin su N5,100, da kuma burodi guda daya na N300.

KU KARANTA: Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

Matar ta bayyana cewa, mai shagon ne ya gano halin da mutumin yake ciki, ba makawa ya kira jami'an 'yan sanda suka kama shi.

Alkalin kotun ya bayyana cewa, sata ta sabawa sashe na 287 na dokar jihar Lagos, kuma hukuncinsa shine shekara uku a gidan yari.

Amma alkalin ya bada belin shi akan kudi N50,000, da kuma shaidu guda biyu.

Daga nan an dage karar har zuwa ranar 26 ga Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel