Jihar Bauchi ba za ta sake goya wa azzalumi baya ba — Dogara

Jihar Bauchi ba za ta sake goya wa azzalumi baya ba — Dogara

- Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara wanda ya jagoranci nasaran zaben jam’iyyar PDP a zaben gwamna a jihar Bauchi, ya bayyana cewa; jihar ta samu ceto daga hannun makiyanta

- Dogara ya jadadda cewa jihar ba za ta sake gigin komawa ga makiyanta ba

- Ya kuma shawarci sabon gwamnan da yayi riko da amanan al’umman jihar Bauchi, kuma ya tuna da rashin amincewa da gwamna mai ci a matsayin darasi

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara wanda ya jagoranci nasaran zaben jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna a jihar Bauchi, ya bayyana cewa; “jihar Bauchi ta samu ceto daga hannun makiyanta, kuma ba za ta taba komawa ga makiyanta ba.”

Yakubu Dogara wanda ya jagoranci jam’iyyar PDP wajen tsige Gwamna mai ci, Mohammed Abdullahi Abubakar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC, ya bayyana cewa “nasarar jam’iyyar na nufin samun makoma nagar, wanda zai amfan yaran da za a Haifa nan gaba a Bauchi.”

Jihar Bauchi ba za ta sake goya wa azzalumi baya ba — Dogara
Jihar Bauchi ba za ta sake goya wa azzalumi baya ba — Dogara
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wani jawabi na musamman dauke da sa hannun shi wanda aka bayyana bayan sanar da dan takaran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Bala Mohammed Abdulkadir a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

KU KARANTA KUMA: Yankin kudu maso gabas na zawarcin kujerar kakakin majalisar wakalai

Kakakin majalisan wanda ya shawarci sabon gwamnan da yayi riko da amanan al’umman jihar Bauchi, kuma ya tuna da rashin amincewa da gwamna mai ci a matsayin darasi har idan suka gaza aiwatar da ayyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel