FG za ta sake waiwayar batun kafa kamfanin jirgin sama na kasa - Sirika

FG za ta sake waiwayar batun kafa kamfanin jirgin sama na kasa - Sirika

- Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sake waiwayan batun kafa kamfanin jiragen sama na kasa

- Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ranar Litinin 25 ga watan Maris

- Sirika ya ce an dakatar da shirin ne domin a daukan wasu matakai kuma nan da kankanin lokaci za a sake waiwayar batun

A ranar Litinin 25 ga watan Maris ne karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce gwamnatin tarayya za ta sake waiwayar batun kafa kamfanin jiragen sama na kasa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ya ruwaito cewa ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke kare kasafin kudin ma'aikarsa a gaban kwamitin majalisar dattawa na sufurin jiragen sama a Abuja.

Gwamnatin Tarayya tayi alkawarin sake bibiyar batun kafa 'Nigeria Air' - Sirika
Gwamnatin Tarayya tayi alkawarin sake bibiyar batun kafa 'Nigeria Air' - Sirika
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

Ya ce ma'aikatan ta dakatar da shirin ne domin daukan wasu matakai kuma nan da kankanin lokaci za a sake waiwayar batun kuma a kafa kamfanin jiragen.

Ya bayyana damuwarsa a kan yadda Najeriya ba ta da kamfanin jirgin sama na kanta duba da yadda ake samun hada-hada da cinikayya a fanin jiragen saman.

Ya ce: "Mun dage shirin kafa kamfanin jiragen sama na kasa ne saboda wasu dalilai na tsare-tsare. Ba an fasa aikin bane. An ware kudade domin wadanda ke bayar da shawarwari a kan aikin su cigaba da aikin domin a cimma nasara.

"Ina tabbatar muku da cewa za a kafa kamfanin jiragen kafin wa'adin wannan gwamnatin ya kare. Gwamnati ba ta manta da batun ba. Za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin anyi nasara."

Sai dai ministan ya ce ba gwamnati kadai bane za ta dauki nauyin kafa kamfanin. "Hadin gwiwa ne za ayi da 'yan kasuwa masu son saka hannun jari. 'Yan kasuwan ne za su jagoranci aikin yayin da gwamnati za ta taka rawar da ya kamata.

Ya ce ma'aikatan a shirye ta ke ta bawa duk wani mai sha'awan saka hannun jari dukkan bayannan da ya ke bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel