Rashin lafiya: An sheka da na hannun-daman Gwamna Ajimobi zuwa asibiti

Rashin lafiya: An sheka da na hannun-daman Gwamna Ajimobi zuwa asibiti

- An kai wasu na kusa-da Gwamna Abiola Ajimobi asibiti bayan sun ci wani abinci

- Hadiman Gwamnan da shugabannin kananan hukumomin jihar sun kamu da cuta

- Hakan ya faru ne bayan Yaran Gwamnan sun halarci bikin kaddamar da kayan aiki

Mutane da dama da su ka halarci bikin kaddamar da wasu manyan motoci na aiki da gwamnatin jihar Oyo ta saya kwanan nan sun kamu da cuta a Ranar Juma’a 22 ga Watan Maris bayan sun ci abinci a wajen wannan taro da aka yi.

Wadanda su ka ci abincin da aka bada wajen kaddamar da wannan kayan aiki sun ruga asibiti bayan cikin su ya birkice. Wadanda wannan abin ya shafa sun hada da manyan gwamnatin jihar Oyo da kuma wasu Sarakunan jihar.

Kamar yadda labari ya zo mana, wani Hadimin gwamnan jihar, da kuma masu kula da kananan hukumomi, da Samuel Eegunjobi, wanda shi yayi takarar mataimakin gwamnan APC a bana, duk su na cikin wadanda cutar ta kama.

KU KARANTA: Buhari ya nuna jimami na wani babban rashi da aka yi a Bayelsa

Bayan wadannan manyan jihar da sauran Magoya bayan APC sun ci abinci ne su ka rika fama da gudawa har aka rika kai su asibiti. Ana zargin cewa wannan abinci da aka raba a wurin taron ne ya batawa mutanen wajen ciki.

Shugaban karamar hukumar Oke-Ogun ya bayyanawa ‘yan jarida cewa yana cin wannan abinci ya ji cikin sa ya fara birkicewa, a karshe dai yace dole yayi ta zarya zuwa ban-daki. Wadannan mutane har sun fara tunanin za su mutu.

Wani ‘dan APC a wurin yace ya shiga kewaye fiye da sau 15 tsakanin Ranar Juma’a zuwa Asabar, sannan kuma yace yayi ta fama da amai akalla sau 6 don haka dole ta kai aka kara masa ruwa a asibiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel