Dalilin da yasa Boko Haram suka kona gidaje a kauyukan Adamawa - Hakimi

Dalilin da yasa Boko Haram suka kona gidaje a kauyukan Adamawa - Hakimi

Hakimin garin Duhu da kewaye a jihar Adamawa, Mohammed Sanusi ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a kauyukan Michika da Madagali da ke kan iyakan Adamawa da Borno a daren Juma'a inda suka kone gidaje sannan suka sace kayayakin abinci a rumbu da shaguna.

Wasu daga cikin mazauna kauyen da suka yi magana da wakilan Punch daga mabuyansu sun ce sun kwana a kan duwatsu ne inda suka kara da cewa 'yan ta'adan sunyi amfani da bindiga wurin razana mutane masu rauni kamar tsofafi da kananan yara.

Har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka kashe ba.

A cewar Sanusi, 'yan ta'addan sun kai farmaki kauyukkan ne saboda ramuwar gayya bayan sojoji sun dakile harin da suka yi yunkurin kai wa a Michika da Madagali kwanaki bakwai da suka wuce.

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

Dalilin da yasa Boko Haram suka kona gidaje a kauyukan Adamawa - Hakimi
Dalilin da yasa Boko Haram suka kona gidaje a kauyukan Adamawa - Hakimi
Asali: Depositphotos

Ya ce harin da 'yan ta'addan suka kai shine na uku a cikin wata daya.

Mazauna kauyen sunyi ikirarin cewa harin yana da nasaba da siyasan jihar bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta bayyana cewa zaben gwamna na jihar bai kammala ba.

Sanusi ya ce, "Mayakan kungiyar Boko Haram sun shigo garin ta kofar Adamawa da kofar Borno misalin karfe 6.30 na yamma inda suka kai hari a cikin dare.

"Sun kone rabin gidajen da ke Kofar Adamawa da kuma dukkan gidajen da ke kofar Borno. Sun shiga cikin kauyukan inda suna barazanar kashe duk wanda ya kallubalance su.

"A lokacin da suka kai hari a Michika mako daya da ya wuce, sun biyo ta kauyukan biyu da suka sabo bi amma sojojin Najeriya da mazauna kauyen sun taka musu birki.

"Ba zan iya tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ba.

"A zuwan da suka yi a baya, sun saka bam a dakin ajiyar kudi na Union Bank amma babu kudi a ciki.

"Sun sace magunguna, man fetur da kayayakin abinci daga kasuwanni da shaguna. Amma da sojoji suka tunkare su, sun tsere sun bar wasu daga cikin motocin su da kayayakin da suka sata.

"Harin da suka kai a ranar Litinin ramuwar gayya ce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel