Yanzu Yanzu: Kotu ta dage umurnin da ya hana sake zaben gwamna a Adamawa

Yanzu Yanzu: Kotu ta dage umurnin da ya hana sake zaben gwamna a Adamawa

Wata babbar kotun Adamawa da ke da zama a Yola ta dage wani umurni da ya hana sake zaben gwamna yiwuwa a jihar.

Kotun ta dage umurnin ne a ranar Talata, 26 ga wataMars biyo bayan rashin gudanar da zabe a mazabu 44 da ke jihar.

Yayinda aka gudanar da zabe a sauran jihohi a ranar Asabar, 23 da watan Maris, ba a gudanar da zabe ba a Adamawa sakamakon karar dadan takarargwamna a jam’iyyar Movement for Restoration and Defence for Democracy (MRDD), Mustafa Shaba, ya shigar akan hukumar zabe.

Yanzu Yanzu: Kotu ta dage umurnin da ya hana sake zaben gwamna a Adamawa
Yanzu Yanzu: Kotu ta dage umurnin da ya hana sake zaben gwamna a Adamawa
Asali: UGC

Shaba ya maka hukumar zabe a kotu kan cire logon jam’iyyarsa a kayayyakin zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babbar kotun Babban Birnin Tarayya a Apo, a ranar Litinin ta kore karar dake zargin gwamna Mohammed Bindow na Adamawa da gabatar da takardun kammala makaranta na bogi ga hukumar zabe ma zaman kanta (INEC) akan rashin iko.

KU KARANTA KUMA: Wasu mutane daga ketare aka kawo su kayi zabe a Kano inji Kwankwaso

Yayinda yake gabatar da hukunci, Justis Olukayode Adeniyi, ya riki kotun da rashin ikon sauraran karan bisa dalilin cewa karar ta zo ne daga jihar Adamawa inda ya kamata a daukaka ta ba a babbar birnin tarayya ba.

Wata kungiya mai zaman kanta, a karkashin kungiyar Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International, ta gabatar da kara kotun inda take zargin gwamnan da mallakar takardun bogi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel