Yankin kudu maso gabas na zawarcin kujerar kakakin majalisar wakalai

Yankin kudu maso gabas na zawarcin kujerar kakakin majalisar wakalai

Kungiyar matasan Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kudu maso gabas, tayi kira ga shugabancin jam’iyyar da ta bai wa yankin mukamin kakakin majalisa a rabe-raben mukamai da za ta yi a majalisar dokokin kasar.

Babban shugaban kungiyar matasan na APC a APC a Kudu gabas, Romanus Oguleme ya bayyana wa manema labarai a Abuja, cewa yankin na da manyan mambobi kuma kwararru a majalissun biyu dake iya shugabantan majalissun.

Ya kara da cewa, kada a fidda yankin daga tsarin shugabancin majalisun kamar yanda ya faru a 2015, inda ya kara da cewa baiwa yankin kudu mukamin kakakin majalisa zai tabbatar tsarin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan alkawarin samar hadin kai a gwamnatinsa.

Yankin kudu maso gabas na zawarcin kujerar kakakin majalisar wakalai
Yankin kudu maso gabas na zawarcin kujerar kakakin majalisar wakalai
Asali: Twitter

Kungiyar tayi korafin cewa dalilin da aka bayar a 2015 na cewa APC a yankin bata da manyan mambobi da za a iya ba manyan mukamai ba zai yi tasiri ba a wannan karon.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta dage umurnin da ya hana sake zaben gwamna a Adamawa

A wani lamari mai kama da haka, mamba mai wakiltan mazabar Arewacin Ezza a majalisar wakilai Anayo Nwonu ya bayyana fatan cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), zata fidda kakakin majalisa.

Nwonu wanda yayi jawabi ga yan jarida a lokacin sake gudanar da zaben majalisan jiha a masabarsa ya bayyana cewa jam’iyyar PDP duk da kasancewar ta mara rinjaye a majalisar ba zai shafi harkokin majalisa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel