Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

A kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take na ganin ta farfado da tattalin arzikin kasar, yanzu haka kasar na bukatar kimanin N10 tiriliyan don gabatar da dukkanin aiyuka na habaka tattalin arzikin kasar

Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola
Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola
Asali: UGC

Ministan aiyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola, ya bayyana cewa Najeriya tana bukatar kudi N10 tiriliyan domin cigaba da aiyukan farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne jiya Litinin a Abuja, lokacin da yake ganawa da 'yan majalisar wakilai, don bayyana yanda aiyukansa suka gudana daga shekarar data gabata zuwa wannan shekarar.

'Yan majalisar wakilan sun yabawa Ministan da irin namijin kokarin da yake wurin kawo cigaba a kasar nan, musamman ma a fannin hanyoyin sufuri.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An soke zaben gwamnan jihar Zamfara tare dana sauran 'yan majalisun jihar da suke jam'iyyar APC

A lokacin da yake bayanin, Ministan ya bayyana cewa kasar nan tana bukatar kudi kimanin N10 tiriliyan, domin cigaba da aiyukan farfado da tattalin arziki.

Ministan kuma ya nuna irin jajircewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ganin an cigaba da aiyukan cigaba a kasar nan, musamman bangaren sufuri.

Shugaban kwamitin majalisar wakilan Toby Okechukwu, ya yabawa Ministan da irin aiyukan da yake yi, inda ya bukaci Ministan ya gabatar da yanda kasafin kudin shekarar nan zai kawo cigaba a fannin sufuri a kasar nan.

A karshe Ministan yayi bayani dalla-dalla, dangane da yanda dukkanin aiyuka suke gudana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel