PDP tayi namijin kokari – Atiku yayi martani ga zaben jihar Bauchi

PDP tayi namijin kokari – Atiku yayi martani ga zaben jihar Bauchi

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a safiyar ranar Talata, 26 ga watan Maris, ya nuna farn cki cewa jam’iyyarsa ta daddake jam’yyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi.

Atiku yace jam’iyyarsa ta tsige APC a Bauchi nda ya bayyana hakan a matsayin wani lamar mai cike da ban al’ajabi.

“Ina taya zababben gwamna, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed murna, wanda ya cikin ban al’ajabi ya kafa tarihi a Bauchi, ya nuna cewa shi mutun ne mai jama’a. Na yi imanin cewa nan shekaru 4 masu zuwa zai nuna cewa shi mutum ne na mutane,” inji shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Bala Mohammed, dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya lashe zaben kujerar gwamna bayan an kai ruwa rana tsakanin sa da gwamna mai ci, Mohammed Abubakar, na jam'iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Manufofin Buhari za su inganta tattalin arziki - APGA

Bayan tattara sakamako da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta yi a yammacin ranar Litinin, an sanar da Bala Mohammed a matsayin wanda ya samu nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Bauchi.

Dakta Musa Dahiru, sabon baturen INEC, ya ce PDP ta samu kuri'u 39,225 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 30,055 daga sakamakon zaben raba gardama da aka yi a jihar Bauchi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel