Zaben Kano: CUPP za ta garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Ganduje

Zaben Kano: CUPP za ta garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Ganduje

Hadakar Jam'iyyun adawa ta ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP), reshen Jihar Kano za ta kallubalanci nasarar da gwaman Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben ciki gibi na gwamna da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

Shugaban CUPP na jihar, Alhaji Muhammad Abdullahi Raji ne ya bayyana hakan yayin da ya ke zantawa da manema labarai a kan sakamakon zaben karo na biyu da aka gudanar inda Ganduje na jam'iyyar APC ya lashe zaben.

Daily Trust ta ruwaito cewa Raji ya ce Hadakar jam'iyyun da ta kunshi jam'iyyun siyasa 42 sun kammala shirye-shirye domin zuwa kotu domin kallubalantar sakamakon zaben.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

Zaben Kano: CUPP za ta garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Ganduje
Zaben Kano: CUPP za ta garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Ganduje
Asali: UGC

Ya ce: "Rahotanni sun nuna cewa anyi ta sayen kuri'u ta razana masu zabe a yawancin akwatunan zaben da aka maimaita zaben. Akwai kuma rahotannin kisa da wasu nau'in magudin zabe da suka faru yayin da jami'an tsaro da na INEC ke kallo.

"Wannan ya nuna karara cewa INEC da hukumomin tsaro ba suyi adalci ba. Bisa ga dukkan alamu rikicin da aka samu a zaben ranar 9 ga watan Maris bai kai wanda aka samu a zaben ranar 23 ga watan Maris din ba amma duk da haka INEC ba ta soke zaben ba.

"Wani babban abin bakin ciki shine batun rashin amfani da na'urar tantance katin zabe wato card reader," inji Raji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel