Manufofin Buhari za su inganta tattalin arziki - APGA

Manufofin Buhari za su inganta tattalin arziki - APGA

Jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) a ranar Litinin, 26 ga watan Maris ta jinjina wa manufofn Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tattalin arziki.

Jam’iyyar tace yan Najeriya zasu fara more ingantacciyar tattalin arziki da wannan kyakyawar manufa na Shugaban kasar.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban jam’iyyar APGA, Victor Oye, yace yan Najeriya su bada goyon bayan su da addu’o’i ga shugaban kasar, inda ya kara da cewa Buhari na bukatan shekaru takwas kamar yanda kundin tsari ta tanadar.

Yayi korafin cewa wassu yan Najeriya suna amfani da lokacin su wajen aibanta shugaban kasar, yayi zargin cewa ba abun ayi ko a mutu bane, kamar yanda yayi nuni ga cewa kwadayin siyasa ke janyo rikicin siyasa a lokacin zabe.

Manufofin Buhari za su inganta tattalin arziki - APGA
Manufofin Buhari za su inganta tattalin arziki - APGA
Asali: Facebook

Ya bukaci yan Najeriya dasu koyi hadin kai da masu rike da mukaman shuwagabanni, inda ya kara da cewa tare da fahimtan ce ake iya samun hadin kai da zaman lafiyan kasa.

KU KARANTA KUMA: Ifeanyi Ubah ya bar jam’iyyar YPP, ya koma APC

Shugaban jam’iyyar ya karfafa bukata ga yan Najeriya dasu bada shawara mai amfani ga shugaban kasa don samun nasara a mulki.

Yayinda yake bayyana ra’ayinsa akan zaben 2019, Oye yace jam’iyyar ta yarda da cewa zaben ya kasance na gaskiya, cewa ko jami’an zabe na kasashen ketare sun tabbatar da haka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel