Idan aka sake zabe sau goma, Atiku zai fadi sau gom

Idan aka sake zabe sau goma, Atiku zai fadi sau gom

- Ko sau nawa Atiku yayi takara da Buhari sai ya taba kasa, cewar BMO

- BMO ta ce Atiku har yanzu bai dawo cikin hayacinsa ba tun bayan fadi a zabe

A ranar Litinin, 25 ga watan Maris, 2019, Kungiyar yada muradun shugaba Buhari, BMO, ta laburta cewa karar da aka shigar domin kalubalantar nasarar Buhari ba zata daure ba saboda babu gaskiya cikinta.

Wannan na kunshe cikin jawabin da shugaba da sakataren kungiyar BMO, Niyi Akinsiju da Cassidy Madueke, suka rattaba hannu.

KU KARANTA: Alkalin kotun koli ya zama sabon sarkin Lafiyan Bare-bari

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar ta ce idan za'a gudanar da zaben shugaban kasa goma, sai Buhari ya lallasa Atiku sau goma.

Tace: "Atiku Abubakar har ila yau bai dawo cikin hayacinsa ba na ganin cewa zai iya kayar da Buhari a zabe."

"Idan aka gudanar da zaben shugaban kasa sau goma, Atiku zai taba kasa sau goma. Atiku ya sani sarai tun kafin a yi zabe cewa ba zai taba iya kayar da Buhari a akwati ba."

"Alamomin sun bayyana karara tun kafin zabe, lokacin zabe da kuma bayan zabe da Buhari ya samu nasara cewa ana sonsa a fadin tarayya. Shi kuma Atiku kiyayyansa tun daga gidansa ta fara bayyana."

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton ceewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyanawa All Progressives Congress (APC) cewa ta shirya fuskantarta a kotun zabe maimakon irin wadannan maganganu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel