Ifeanyi Ubah ya bar jam’iyyar YPP, ya koma APC

Ifeanyi Ubah ya bar jam’iyyar YPP, ya koma APC

- Zababben sanata Ifeanyi Ubah ya sauya sheka daga jam’iyyar YPP zuwa APC

- Lamarin na zuwa ne kwanaki hudu bayan Ubah ya karyata rahotannin cewa yana shirin sauya sheka

- Shugaban jam'iyyar APC, Adams Osiomhole ne ya sanar da sauya shekar Ubah a wani taron tattaunawa da sanatoci da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a fadarsa da ke Abuja

Bayan lashe zaben sanata mai wakiltan kudancin Anambra a jam’iyyar Young Peoples Party (YPP), Ifeanyi Ubah ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan ya musanta rahotannin cewa yana shirin sauya sheka.

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana komawar Ubah zuwa jam’iyya mai mulki a wani taron tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da sanatocin APC a fadar shugaban kasa a daren ranar Litinin, 26 ga watan Maris.

Ifeanyi Ubah ya bar jam’iyyar YPP, ya koma APC
Ifeanyi Ubah ya bar jam’iyyar YPP, ya koma APC
Asali: Depositphotos

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Akinwumi Ambode (Legas), Nasir el-Rufai (Kaduna), Yahaya Bello (Kogi), Simon Lalong (Plateau), Atiku Bagudu (Kebbi) da Abdulaziz Yari (Zamfara).

KU KARANTA KUMA: Osun: Dallin da yasa Adeleke ba zai iya samun takardar shadar cin zabe ba a yanzu – INEC

Sauran sun hada da Abubakar Badaru Abubakar (Jigawa), Ibrahim Gaidam (Yobe), Kashim Shetima (Borno) da Gboyega Oyetala (Osun).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel