Ndume ya shiga sahun masu neman shugabancin majalisar dattawa

Ndume ya shiga sahun masu neman shugabancin majalisar dattawa

Tsohon Jagora a Majalisar Dattawa, Sanata Muhammed Ali Ndume ya sanar da niyyarsa na shiga sahun wadanda za suyi takarar kujerar shugaban majalisar dattawa karo na tara.

Ndume yana neman albarka da amincewar shugabanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne domin shiga takarar.

Sanatan da ya fito daga Kudancin Borno shine dan takara na biyu da ya nuna sha'awarsa na shiga sahun masu neman takarar kujerar shugabancin majalisar.

Sanata Ahmed Lawan shine mutum na farko da ya fara nuna sha'awar takarar shugabancin majalisar kuma bisa ga dukkan alamu ya samu goyon bayan jiga-jigan jam'iyyar.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

Ndume ya shiga sahun masu takarar shugabancin majalisar dattawa
Ndume ya shiga sahun masu takarar shugabancin majalisar dattawa
Asali: UGC

Ndume ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne saboda yana kyautata zaton daga yankinsa ne za a fitar da shugaban majalisar a wannan karon.

A wasikar da ya aike wa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole a ranar 25 ga watan Maris, ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne saboda niyyarsa na bayar da gudunmawa wurin zartar da ayyukan cigaban al'umma a kasar.

"Bayan nasarar da aka samu na gudanar da zaben 2019 da nasarorin da jam'iyyar APC ta samu a matakai daban-daban, ina son in mika wasikar nuna sha'awa ta na shiga takarar shugabancn majalisar dattawa karo na tara.

"Ina son jadada cewa na yanke shawarar shiga takarar ne saboda niyya ta na bayar da gudunmawa ta wurin gina kasa," kamar yadda ya fada a wasikar.

A baya, Ndume ya rike mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya karo na shida kuma daga bisani ya rike mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa karo na takwas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel