Zan tafiyar da gwamnati na ta yadda babu wanda zai juya ni - Tambuwal

Zan tafiyar da gwamnati na ta yadda babu wanda zai juya ni - Tambuwal

- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ba wa mutanen jihar tabbacin cewa, babu mai juya shi a mulkinsa na biyu

- Tambuwal ya sha alwashin yin aiki ba kakkautawa domin ya sabonta yardar da mutane suka yi da gwamnatinsa a jihar

- Zababben gwamnan ya kuma musanta batun amsa kra daga Sanata Wamakko da dan takarar APC a jihar, Ahmed Aliyu, sannan yayi kira a gare su da su zo suyi aiki domin ci gaban jihar

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a jiya, Litinin, 25 ga watan Maris ya ba wa mutanen jihar tabbacin cewa, babu mai juya shi a mulkinsa na biyu.

“Zan gudanar da gwamnatin da wani ba zai juya ni ba,” inji shi, yayinda yake zantawa da manema labarai a Sokoto.

Ya bayyana cewa ba zai taba manta nasarar da yayi da kuri’u 342 ba. “Aikin Allah ne idan aka duba abunda ya faru a lokacin zabe,” cewar shi.

Zan tafiyar da gwamnati na ta yadda babu wanda zai juya ni - Tambuwal
Zan tafiyar da gwamnati na ta yadda babu wanda zai juya ni - Tambuwal
Asali: UGC

Ya sha alwashin yin aiki ba kakkautawa domin ya sabonta yardar da mutane suka yi da gwamnatinsa a jihar.

Ya karyata batun amsa kowani kiran waya daga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da dan takarar gwamna na jam’iyar All Progressives Congress (APC), Ahmed Aliyu, da ke cewa sun taya shi murna akan nasarar da yayi.

Ya yi kira a gare su, cewa ana bukatar goyon bayansu wajen ci gaban jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta farko a tarih da ta nada kwamishinoni mata uku, sakatarorin din-dn mata takwas da kuma kansiloli mata uku-uku a dukkanin kananan hukumomi 23.

KU KARANTA KUMA: Osun: Dallin da yasa Adeleke ba zai iya samun takardar shadar cin zabe ba a yanzu – INEC

Ya kara da cewa gwanatinsa na kashe naira miliyan 120 duk wata domin siyan ssinadarn tsaftace ruwa.

Tambuwal yace gwmnatinsa na aki tare da majalisar Sultan, shugabannin garuruwa da kuma hukumomin tsaro wajen magance ta’addanci a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel